‘yan sara suka sun kai farmaki ga ‘yan majalisar jihar Bauchi

Bauchi State Assembly 0
Bauchi State Assembly 0

‘yan daba sun kai wa ‘yan majlisar Bauchi hari a gidan saukar bakin su dake jihar ta Bauchi, yayin harin sun lalata motoci da wunduna a gidan.

Jaridar solacebase ta rawaitu cewa mjalisar tana cikin rigima tun ranar Alhamis data wuci, sakamakon ‘yan majalisar 22 sun marawa shugaban majalisar Abubakar Sulaiman baya.

Shugaban masu rinjaye na majasir, Babale Abubakar ya shaidawa manema labarai cewa harin ya faru ranar Alhamis da misalin karfe 4 na yamma, dai dai lokacin da ‘yan majalisar suke ganawa a gidan saukar baki na ‘yan majalisar.

Mai taimakawa gwamnan jihar kan al-amuran tsaro, ya bikaci jami’an tsaro suyi binkice akan wadan da ke da hannu akan kai harin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here