Shugaban Najeriya mai barin gado Muhammadu Buhari yace zai bar Najeriya cikin kyakkyawan yanayi fiye da yadda ya karɓe ta lokacin da ya hau karagar mulkin kasar a shekarar dubu biyu da goma sha biyar.
Buhari ya bayyana hakan ne da safiyar ranar Lahadi lokacin da yake gabatar da jawabinsa na ƙarshe a matsayin shugaban kasar, yayin da ya rage kwana guda a rantsar da sabon Zaɓaɓɓen shugaban kasar nan mai jiran gado wato Asiwaju Bola Adekunle Ahmad Tinubu.
Shugaba Buhari ya mika godiya ga duk wadanda suka ba da goyon baya da karfafa masa gwiwa wajen ciyar da Najeriya gaba.
“Ina kuma so in yi amfani da wannan dama domin in nuna godiyata ga dimbin ‘yan Najeriya Maza da Mata waɗanda suka ba da goyon baya tareda karfafa min gwiwa wajen gudanar da aikin da ya rataya a wuya na matsayin shugaban kasar nan don ciyar da ita gaba.
“Ba zan iya mantawa da miliyoyin mutanen ƙasar nan da suka yi mini addu’a a lokacin da nake rashin lafiya tun a wa’adin zangon mulkina na farko. Ina yi muku fatan Alkhairi da addu’a a kodayaushe, Allah ya karawa Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali da yauƙaƙar tattalin arzikin ƙasa.
“Yayin da na kammala shugabancin kasar nan zan koma gidana dake Daura, a Jihar Katsina, ina mai farin ciki da jin dadin cewa mun ɗora Nijeriya akan hanyar da ta dace, kuma ina da yakinin gwamnati mai zuwa za ta ɗora daga inda muka tsaya don ganin ƙasar ta kai ga ci.
A yayin jawabin na Shugaban ƙasar mai barin gado ya jera wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Da yake bayani kan tattalin arziƙi, shugaba Buhari ya ce “Tattalin ariziƙinmu ya ƙara bunƙasa sakamakon irin matakan da aka ɗauka domin ganin cewa bai durƙushe ba a lokacin da dai-dai lokacin da tattalin arziƙin duniya ya shiga mummunan hali.”
Ya ƙara da cewa “A ƙoƙarin inganta tattalin arziƙin mun ɗauki matakai masu matuƙar wahala waɗanda yawancinsu suka samar da sakamako mai kyau.”
“Wasu daga cikin matakan sun haifar da wahalhalu, kuma ina mai neman afuwar al’ummar ƙasa game da hakan. Sai dai mun ɗauki matakan ne domin amfanin wannan ƙasa.”
Shugaba Buhari ya ƙara da cewa “Ƴan uwana ƴan Najeriya kun san yadda, har cikin zuciyata nake matukar so na ga na yaƙi rashawa wanda shi ne ya hana ƙasar nan ci gaba. Na yi iya bakin ƙoƙarina wajen ganin an ci nasara duk da irin turjiyar da muka samu wadda da ma mun yi tsammanin hakan.”
“Ina matuƙar farin ciki kan cewa an samu nasarar ƙwato maƙudan kuɗaɗe daga wajen waɗanda suka handame zuwa wasu ƙasashen duniya an kuma dawo da su gida, Kazalika an ƙwace kadarorin da aka saya da kuɗin haram”
A batun tsaro kuwa shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi iyakar bakin ƙoƙarinta, inda ta samu nasarar “rage kaifin ayyukan ƴan bindiga da ta’addanci da fashi da makami da Boko Haram da sauran ayyukan ɓatagari”
Buhari ya kuma buƙaci al’ummar Najeriya su kasance masu taimaka wa jami’an tsaro ta hanyar lura da abubuwa da ke faruwa a yankunansu domin ganin an ɗora kan nasarar da gwamnatinsa ta samu.
Ya kuma ce “Har yanzu ina takaicin yadda ake ci gaba da garkuwa da yaranmu. Ina jajanta wa iyaye da abokai da ƴan uwan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunar ta’adda da tashin hankali.
Jami’an tsaronmu na aiki ba dare ba rana domin ganin sun karɓo waɗanda har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.”
Muhammadu Buhari ya ƙara da cewa ya yi iyakar bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya sauke nauyin da ya ɗauka na mulkin ƙasar nan, kuma zai ci gaba da yi wa ƙasar addu’a bayan sauka daga mulki.













































