Ganduje Zai Mika Mulki Yau, Domin Halartar Bikin Rantsar Da Tinubu 

Ganduje sad
Ganduje sad

Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje zai mika ragamar kula da harkokin jihar ga zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf a ranar Lahadi. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai da harkokin cikin gida, Muhammad Garba, ya fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu a garin Kano.

Mista Garba ya bayyana cewa ana sa ran taron zai gudana da misalin karfe 9:00 na daren ranar 28 ga watan Mayu a gidan gwamnatin Kano.

A cewarsa, kwamitin mika mulki na gwamnatin jihar ta sanar da ci gaban ga kwamitin mika mulki na zababben gwamnan.

Ya kuma bayyana cewa kwamitocin biyu sun gana cikin makon yayin da aka gabatarwa kwamitin zababben gwamnan da takardun mika mulki sannan an yi aiki kan ajandar bikin mika mulkin.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa jim kadan bayan taron Ganduje zai tafi Abuja a matsayin shugaban tawagar Kano zuwa bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a ranar Litinin. Ya kara da cewar tafiyar gwamnan ya zama dole ne don yin daidai da wa’adin rufe filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin bikin rantsar da shugaban kasar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here