Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, ya hallara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin domin sauraron kararsa bayan kotun ta bayar da umarnin kama shi.
Sowore, wanda kuma shi ne mawallafin Jaridar Sahara Reporters, ya isa kotun tare da mambobin kungiyarsa dauke da allunan.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Mai Shari’a Mohammed Umar, a ranar 16 ga Yuni, ya soke belin da aka bayar na Sowore saboda rashin hallara kotu dominn sauraron karar sa.
Mai Shari’a Mohammed Umar, a cikin hukunci kan rokon da lauyan Hukumar Tsaro ta DSS, Akinkolu Kehinde SAN ya yi, ya kuma ba da umarnin kama Sowore.
DSS tana gurfanar da Sowore kan zargin shi da yin zarge-zargen karya kan Shugaba Bola Tinubu ta hanyar kiran shi “mai laifi” a cikin rubutun da ya yi a shafinsa na “X” da Facebook.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kotu ba ta fara zama ba. NAN











































