Kwara: Kudurin gyaran doka kan hana samar da gawayi ya tsallake karatu na biyu

Charcoal 750x430

Majalisar Dokokin jihar Kwara ta amince da kudurin gyaran dokar hana samar da gawayi na shekarar 2025 a karatu na biyu a zauren majalisar da ke Ilorin.

Kudurin, wanda shugaban kwamitin muhalli na majalisar, Razaq Omotosho (APC/Isin) ya dauki nauyi, ya yi nufin ƙarfafa dokokin da ake da su ta hanyar tsaurara hukunci ga masu hannu a samar da gawayi ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa an karanta kudurin a karatu na farko a ranar 9 ga Satumba, lokacin zaman majalisar.

Yayin tattaunawa kan kudurin a zaman Talata, Omotosho ya bayyana cewa an kawo gyaran domin farfado da tsarin muhalli da ke fuskantar barazanar bacewar dabbobi da tsirrai sakamakon sare itatuwa ba tare da shuka sabbi ba.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta haramta yin Muƙabala tsakanin Sha’irai ba tare da izini ba, ta umarci wasu Sha’iran su bayyana gabanta

Ya ce masu sare itace na amfana da aikin amma suna barin al’umma da muhalli cikin hadari.

Ya jaddada cewa ceto muhalli na bukatar hadin kai, in ba haka ba tattalin arzikin jihar da rayuwar jama’a za su shiga cikin mawuyacin hali na lalacewar muhalli da asarar rayuka. Ya ce tsauraran hukunci ne kadai za su zama izina ga masu karya doka.

Wasu ‘yan majalisar sun nuna cewa samar da gawayi ba bisa ka’ida ba ya taimaka wajen lalata dazuzzuka, haifar da sauyin yanayi, cututtuka da kuma rasa kudaden shiga na jihar. Sun ce sabon kuduri zai kawo karin tsawon zaman kurkuku, tarar kudi mai yawa da kuma kwace kayan aikin masu laifi domin kare muhalli.

A nata jawabin, Rukayat Shittu (APC/Owode Onire) ta ce akwai gaggawar gyara doka kasancewar dokar 2018 ta kasa dakile masu ci gaba da sare itatuwa. Ta nemi a gaggauta amincewa da kudurin, inda ta nuna cewa samar da gawayi ya lalata yanayi tare da kawo sauye-sauyen yanayi da yanayin zafi a jihar.

Shi ma Ayi Babatunde (APC/Ilorin West) ya ce hukuncin da ke cikin dokar yanzu ba ya da karfi, saboda haka akwai bukatar gyara. Ya ce dokokin yanzu ba su da tasiri wajen dakile matsalar.

A karshe, Kakakin majalisar, Yakubu Danladi-Salihu, ya umurci magatakarda na majalisar, Alhaji Ahmed Kareem, da ya karanta kudurin a karatu na uku, sannan ya tura shi zuwa kwamitin muhalli don ci gaba da aiwatar da matakan da suka dace sannan a kawo rahoto cikin gaggawa.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here