Gamayyar hadin gwiwa ta kungiyar ma’aikatan hukumar ‘yan sanda sun tsunduma yajin aikin sakomakon wani rikici da ya barki kan daukar ma’aikata da hukumar zata yi.
Kunigyar ta ce yajin aikin zai fara aiki daga ranar Litinin 29 ga watan Agusta na shekarar 2022.
Shugaban kongiyar, Mista Adoyi Adoyi, ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da jaridar Punch ranar Alhamis.
Barazanar yajin aikin na zuwa ne ya yin da ake ta kai ruwa rana tsakanin hukumar ta ‘yan sanda da kuma babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Usman baba, kan daukar ma’aikata da kuma kara musu girma.
Shugaban kungiyar ya zargi babban sifeton da yiwa kudin dokar hukumar karan tsaye.













































