Rundunar sojojin Najeriya zata bawa sojoji mata horo

Army obirin 750x430 1
Army obirin 750x430 1

Rundunar sojojin Najeriya ban garen mata (NAWC), za su fara karbar horo na kwana 7 daga ranar 27 ga watan Agusta zuwa 2 ga watan Satumba, a garin Giri-Gwagwalada da ke babban birnin tarayya Abuja.

Za’a bawa sojoji mata horon ne domin kara inganta kwarewar su da kuma tabbatawa suna shirye domin fara tura su duk wani aiki da za’ai tare da abokanan aikin su maza.

Rundunar ta yi kira ga mazauna garuruwan Gwagwalada, Giri, Tugan Maji, Ana-Gada, Gudumba, Tagilogo da kuma Makalma da ke Abuja, indan sunga motsin sojoji su kwantar da hankalin su.
Sanan kuma rundunar ta kira yin ga mazaunan da su cigaba da harkokin su na yau da kullum, su kuma kauracewa goraren da za’a bada horon.

Sanarwa: Kaftin HASHIMU SA’AD ABDULLAHI.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here