YANZU-YANZU: EFCC ta bada belin tsohon gwamnan Anambra Obiano

download
download

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Anambra Willie Obiano.

Shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana hakan yau litinin lokacin da yake tattaunawa da da manema labarai a Abuja, a wajen taron shekara na kungiyoyin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na yammacin Afrika.

Sai da Bawa yace, kawo yanzu Obiano bai cika sharudan bayar da beli da aka gindaya masa ba, don haka har yanzu yana tsare a hannun hukumar har sai ya cika sharudan.

A ranar alhamis din da ta gabata ne da misalin karfe 8:30 na dare hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan na Anambra a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Legas a kan hanyar sa ta zuwa kasar Amurka.

Daga bisa aka kai shi hedkwatar hukumar dake Abuja, inda ake zarginsa da almundahanar kudin da suka kai naira biliyan arba’in da biyu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here