Lauya, Peter Oyewole, a ranar Laraba, ya shaida wa kotu cewa tsohon shugaban hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, Farfesa Adedibu Ojerinde, ya mallaki wasu kamfanoni na bogi guda 8.
Oyewole ya kuma shaidawa Mai Shari’a Obiora Egwuatu cewa Ojerinde ya dauke shi a matsayin lauyansa a lokacin da yake rike da mukamin shugaban hukumar JAMB.
Ya bayyana hakan ne yayin da lauyan hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC), Ebenezer Shogunle yake gabatar da shi a matsayin shaida.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, lauyoyin masu gabatar da kara da kuma wadanda ake kara, a ranar Talata, sun yi bukaci kotun da ta baiwa bangarorin biyu karin kwana daya don gudanar da wani shiri na sasantawa.
Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar Laraba domin karbar rahoto kan karar.
Sai dai kuma a lokacin da aka ambaci karar da safiyar yau, babban lauya mai shigar da kara, Ebenezer Shogunle, ya shaida wa kotun cewa sulhun da aka shirya a wajen kotu ya ci tura.
Oyewole ya shaida wa kotun cewa Bayanin A na kunshe da jerin kamfanoni da kadarori da wanda ake kara ya mallaka
‘Shaidar B da B1 sun ƙunshi jerin sunayen kamfanoni da na yi rajista a madadin wanda ake tuhuma da kuma kadarorin da wanda ake tuhuma ya saya,” in ji shi.
Ya lissafa kamfanonin da suka hada da OKeafin Boys and Girls Hostel Ltd, Shapatti International School, Doyin Ogbohi Petroleum Ltd, Cheng Marbles Ltd, Standout Institute Ltd, Trillium Learning Center School, Grace Petroleum Ltd, Ifelodun Communications Ltd, da dai sauransu.
Ya ce Ojerinde ya umarce shi da ya yi wa kamfanonin rajista kuma ya mallaki kadarorin a madadin sa.













































