Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Zamfara, ta kama buhuna 9 dauke da 450kg na duwatsu masu daraja daga hannun masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Rundunar ta kuma ce ta kama babura takwas, tare da kama wata karamar bindiga, tare da kama mutane 10 da ake zargi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mista Ikor Oche, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a Gusau ranar Laraba.
Oche ya ce: “A bisa bayanan sirri, rundunar ta tura tawagar ma’aikata zuwa wurin da ake hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma cibiyar da ake sarrafa kayayyakin hakar ma’adanai zuwa kayyaki.
“Bakwai daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne a cibiyar hakar ma’adanai, yayin da sauran ukun kuma an kama su a cibiyar sarrafa su da ke yankin Matusgi a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar.”
Ya ci gaba da cewa biyu daga cikin ma’aikatan da suka jikkata a yayin kamen a halin yanzu suna karbar magani a gidajensu.
“Hukumar hana hakar ma’adanai a jihar har yanzu tana aiki.
“Saboda haka, duk mutumin da aka samu a aikin hakar ma’adinai, za a hukunta shi da gaske,” in ji shi.
Don haka Oche ya shawarci jama’a da su nisanci hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba domin rundunar tana aiwatar da dokar hana ta kuma a shirye take ta tunkari duk wani mai karya doka daga yanzu.












































