TETFund ta tallafawa jami’ar ATBU da Naira biliyan 15 don gudanar da ayyuka  

Abubakar Tafawa Balewa University
Abubakar Tafawa Balewa University

Asusun kula da manyan makarantu (TETFund) ya samar da Naira biliyan 15 ga Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake Jihar Bauchi a cikin shekaru 10 domin gudanar da ayyuka.

Farfesa Ahmed Abdulaziz, shugaban jami’ar ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a wata hira da yayi a Bauchi ranar Alhamis.

Abdulaziz cewa ayyukan sun hada da gina Babban dakin gwaje-gwaje; Kwalejin Kimiyya (Mataki na II); Clinical Complex, College of Medicine, ATBU Teaching Hospital; da Cibiyar Kimiyya, Fasaha da Ci gaban Harkokin Kasuwanci.

Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya da TETFUND da suka samar da asusun gudanar da ayyukan, inda ya kara da cewa idan ba don asusun ba, da dukkanin jami’o’in Najeriya sun durkushe.

Shugaban jami’ar y ace sun bullo da karin kwasa-kwasan karatun digiri na farko da na biyu da na uku saboda samuwar gine-ginen da za su iya daukar nauyin yawan daliban.

Hukumar TETFund wata hukuma ce da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa domin kawo gyara a fannin ilimi, wanda ya kama hanyar lalacewa saboda rashin kayan koyo da koyarwa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here