Kashi 95 na masu akidar Boko Haram basa raye – Gwamnatin Borno

'Yan bindiga, Kujuru, mata, sace, hari
‘Yan bindiga sun sake kai wani sabon hari garin Banono da ke karkashin masarautar Kufana ta karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a tarayyar Najeriya,..

Gwamnatin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ta yi ikirarin cewa kashi 95 cikin 100 na masu ra’ayin Boko Haram ba sa raye a yanzu musamman jagororin farko da suka assasa tafiyar kungiyar.

Mashawarci na musamman ga gwamnatin jihar Borno kan sha’anin tsaro Birgediya Janar Ishaq Abdullahi mai ritaya ya ce galibin masu ra’ayin na Boko Haram ko dai sun mutu ko kuma sun mika wuya ga hukumomi.

Karin labari: Kar ku baiwa jami’ai cin hanci – Tinubu

A cewar Janar Abdullahi, kashi 10 na masu akidar Boko Haram ne kadai suka yi saura yanzu haka a Najeriya dai dai lokacin da jami’an tsaro ke ci gaba da fatattakar barazanar tsaron da yankin na arewa maso gabashin Najeriya ke fuskanta.

Janar Abdullahi ya bayyana cewa kaso mai yawa na kwamandojin Boko Haram sun mutu ne a yakin da ya barke tsakaninsu musamman bayan rabuwar kungiyar zuwa tsagi biyu wato ainahin kungiyar ta Boko Haram da kuma ISWAP mai biyayya ga IS.

Karin labari: Sudan ta buƙaci a mayar da ita AU kafin ta amince shiga tsakanin ƙungiyar

Mashawarcin gwamnatin kan harkokin tsaro ya kafa hujja da kalaman wani babban kwamandan Boko Haram wanda ke cewa cikin su 300 da suka faro tafiyar kungiyar a 2009 yanzu haka babu adadin da ya kai mutum 10 kuma su kansu sun fantsama sassa daban-daban saboda rikicin shugabanci a tsakaninsu.

A cewar jami’in kaso mai yawa na mayakan Boko Haram sun mutu sanadiyyar Harbin maciji bayan da suka fantsama dazuka, wasun su kuma sun mutu sakamakon hare-haren Sojin Najeriya wadanda ko dai suka mutu nan take ko kuma suka gudu da raunuka daga bisani suka mutu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here