Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji ya bayyana cewa zai tsaya takarar gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2023 wanda ke kara matsowa.
Solacebase ta ruwaoto cewa Alhaji Usman Alhaji, wanda kuma shine wazirin masarautar Gaya ya bayyana hakan ne a wajen wani taro da kungiyar Patriotic Volunteers for Good Governance ta shirya, wanda aka gudanar ranar Lahadi a Kano.
Yace “Shekaru 6 ana damawa dani a gwamnatin kano,dan haka ni na fi dacewa na gaji kujerar gwamnan jihar Kano, a zaben 2023”
Ya kara da cewa Kano tana bukatar wanda zai dora kan ayyukan alkairi da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya fara, yana mai cewa idan aka bashi dama zai kasara ayyukan gwamna Ganduje tare da kirkiro sabbin ayyuka.
“Abu ne dana roka, idan Allah ya bani dama za’a yi gaskiya a harkar gwamnati, za’a yi ayyuka don ci gaban al’umma saboda Allah, ba don son ran wani ba ko cikar burin wani.” Inji shi.













































