Shugaban kasa Bola Tinubu ya rubuta wasiku biyu zuwa majalisar Dattawa yana neman amincewa da sunayen mutane 21 da ya zaba domin shiga kwamitocin hukumar kula da harkokin man fetur da ƙayyade farashi ta kasa NMDPRA da kuma hukumar kula da harkokin hako man fetur ta kasa NUPRC.
A wasikar farko, Shugaba Tinubu ya zabi Sanata Magnus Abe domin zama shugaban kwamitin hukumar NUPRC.
Abe ya taba wakiltar mazabar Rivers ta kudu maso gabas a majalisar Dattawa na wa’adi biyu, kuma tsohon mamba ne a kwamitin NNPC, tare da kasancewa shugaban hukumar kula da ganuwar kore ta kasa a halin yanzu.
Sauran wadanda aka zaba domin kwamitin NUPRC sun hada da Injiniya Paul Yaro Jezhi, tsohon shugaban kungiyar Trade Union Congress a Kaduna, da Sunday Adebayo Babalola, tsohon mataimakin darakta a sashen DPR wanda dokar PIA ta rusa a shekarar 2021.
Wadannan biyun za su yi aiki a matsayin kwamishinoni marasa zartarwa, yayin da aka kuma zabi kwamishinonin zartarwa da dama domin sassa daban-daban na hukumar.
Daga cikin kwamishinonin zartarwa da aka zaba akwai Muhammed Sabo Lamido a bangaren kudi, Edu Inyang a bangaren bincike da filayen hako mai, Justin Ezeala a bangaren tsare-tsaren tattalin arziki da tsari, Henry Darlington Oki a bangaren ci gaba da samarwa, Indabawa Bashari Alka a bangaren ayyukan kamfani da gudanarwa, Mahmood Tijani a bangaren lafiya, tsaro da muhalli, yayin da Olayemi Adeboyejo zai kasance sakatare da mai ba da shawarar shari’a.
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya nada Lamido da Adeboyejo a shekarar 2022, yayin da shi kuma ya nada Alka a shekarar 2023.
Wasu daga cikin wadanda aka ambata kamar Inyang, Ezeala, Tijani, Babalola da Jezhi sabbin nade-nade ne na Shugaba Tinubu.
A wasika ta biyu zuwa majalisar dattawa, Shugaba Tinubu ya zabi Adegbite Ebiowei Adeniji a matsayin shugaban kwamitin hukumar NMDPRA.
Adeniji lauya ne mai fiye da shekaru 30 na gogewa a harkokin makamashi da albarkatun kasa, inda ya taba zama mai ba da shawara ta musamman ga karamin ministan man fetur, sannan ya yi aiki da bankin duniya kan gyaran bangaren man fetur a Najeriya.
Sauran wadanda aka zaba domin kwamitin NMDPRA sun hada da Kenneth Kobani da Asabe Ahmed a matsayin mambobi marasa zartarwa, da Abiodun Adeniji, Francis Ogaree, Oluwole Adama da Mustapha Lamorde a matsayin daraktoci masu zartarwa.
Shugaban kasa ya bukaci majalisar dattawa da ta hanzarta amincewa da wadannan nade-nade, tare da bukatar dukkan wadanda aka zaba su gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da gaskiya a matsayin masu kula da bangaren mai da iskar gas na kasa.












































