Kotun tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar beli da Yakubu Adamu, kwamishinan kudi na jihar Bauchi, ya gabatar tare da sauran wadanda ake tuhuma bisa zargin daukar nauyin ta’addanci da ya kai dalar Amurka miliyan 9.7.
Mai shari’a Emeka Nwite ya yanke hukuncin cewa laifuffukan da ake tuhumar wadanda ake kara da su suna barazana ga tsaron kasa da lafiyar jama’a, yana mai cewa laifukan da suka shafi ta’addanci na lalata tsarin zamantakewa, kuma sakin wadanda ake tuhuma kafin shari’a na iya jefa al’umma cikin hadari.
Kotun ta bayyana cewa duk da tanadin sashe na 36(5) na kundin tsarin mulki wanda ke tanadar da daukar mutum a matsayin marar laifi har sai an tabbatar da laifinsa, wannan tanadi ba ya aiki kai tsaye ba tare da la’akari da wasu muhimman abubuwa ba, musamman a lokacin duba bukatar beli.
Mai shari’a ya yi nuni da hukuncin kotun koli na baya wanda ya bayyana cewa wajibi ne a duba irin laifin da ake tuhumar sa da shi, karfin hujjojin da ke gabansa da kuma tsananin hukuncin da ka iya biyo baya idan an samu mutum da laifi, yana mai cewa wadannan abubuwa ba za a yi watsi da su ba.
Kotun ta ce bayan duba shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar, ciki har da bayanan shaidu da kuma barazanar da lamarin ke haifarwa ga tsaron kasa, an samu dalilan da ke nuna yiyuwar alhakin laifi a kan wadanda ake tuhuma, don haka bukatar beli ba ta dace ba a wannan mataki ba.
Sai dai kotun ta bayar da umarnin gaggauta sauraron shari’ar domin tabbatar da adalci ga bangarorin da abin ya shafa, tare da dage sauraron shari’ar zuwa wani lokaci na gaba domin fara cikakken shari’a.
NAN













































