Rikicin jihar Rivers: Wike ya yi barazanar  daukan mataki a kan sakataren APC na ƙasa, Basiru

Nyesom Wike Minister of FCT 640x430

Ministan babban birnin tarayya FCT, Nyesom Wike, ya gargadi sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Basiru, da ya nisanci harkokin siyasar Jihar Rivers tare da kaurace wa kalamai da ka iya tayar da hankali game da jihar.

Wike ya bayar da wannan gargadi ne yayin ziyarar godiya da ya kai karamar hukumar Oyigbo, inda ya bayyana cewa wasu ’yan siyasa sun yi anfani da abin da aka ce kudade masu yawa sun rage a baitulmalin jihar, suka fara yin maganganu marasa tushe kan harkokin Rivers.

Gargadin ya biyo bayan wasu kalamai da aka danganta ga mataimakin shugaban APC na shiyyar Kudu maso Kudu, Victor Giadom, wanda ya nuna rashin girmamawa ga Gwamna Siminalayi Fubara a wasu ziyarce-ziyarcen baya da aka kai yankunan kananan hukumomin Khana da Gokana.

Bayan haka, Ajibola Basiru ya bayyana cewa irin wadannan kalamai ba su dace ba, yana mai jaddada cewa mukamin gwamna na bukatar a girmama shi komai banbancin siyasa da ke akwai.

Wike ya mayar da martani da gargadi mai tsauri, yana mai bayyana cewa Jihar Rivers ba za ta amince da tsoma baki daga waje ba, tare da kira ga Basiru da ya dauki darasi daga abin da ya faru ga wasu da suka taba kokarin yin irin wannan tsoma bakin a baya.

A bangare guda, jakadan shirin sabunta manufa “Renewed Hope” na Jihar Rivers, Desmond Akawor, ya dora laifin tsaikon ci gaba a karamar hukumar Oyigbo kan Gwamna Fubara, yana mai cewa al’ummar yankin sun kada kuri’a ne da fata mai yawa amma ba su ga wani gagarumin ci gaba ba tun bayan hawansa mulki.

Akawor ya kara da cewa al’ummar Oyigbo ba sa neman wata fifiko ta musamman, sai dai adalci da rabon ci gaba yadda ya dace, tare da cewa yankin bai kamata a bar shi a baya ba a duk wani shiri ko rabon albarkatu na jihar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here