Gwamnatin Kano ta dauki matasa 600 don su samu horo kan yakar laifukan a cikin birane

Abba Kabir Yusuf Yusuf 750x430

Gwamnatin Jihar Kano ta fara horas da matasa 380 a matsayin rukuni na farko na wani shiri da aka kaddamar domin dakile matsalolin satar wayoyi, ta’addanci na tituna da sauran laifuka a cikin birane.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a da wayar da kai na ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyuka na musamman, Muhd Dahir Idris, ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta bayyana cewa matasan suna daga cikin masu aikin sa kai 600 da aka tanada domin zama jami’ai na musamman da za su yaƙi ayyukan ƙwacen waya Special Antiphone Snatching da sauran kalubalen tsaro.

An fara yi musu horo na makonni biyu a cibiyar tsaro ta jihar da ke Gabasawa, inda za su samu kwarewa da horon ladabtarwa domin tallafa wa hukumomin tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Kwamandan cibiyar, Kyaftin Muhammad Bello Mai Gaskiya (rtd), ya ce shirin na ba da horo kan dabarun hana satar wayoyi, kare manyan baƙi, tuki cikin kariya, motsa jiki, atisayen tsaro, da kuma tarukan ba da shawarwari.

Labari mai alaƙa: Samar da ƴan sandan jiha hanya ce ta jawo rikici – Tsohon AIG Adisa Bolanta Tsohon

Haka kuma, jami’an hukumar yaki da miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) da hukumar Hisbah za su ba da darussa a wannan shiri.

Ya bukaci matasan da su dage da jajircewa a lokacin shirin, yana mai cewa rawar da za su taka za ta zama muhimmiyya wajen dawo da tsaro a cikin al’ummomin Kano.

Bayan kammala horon, gwamnati za ta karɓe su a hukumance tare da basu albashi na kowane wata.

Sanarwar ta kuma tunatar da cewa a karshen mako da ya gabata, kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman, Air Vice Marshal Ibrahim Umaru (rtd), ya duba cibiyar horaswar Gabasawa, inda ya tantance ofisoshi, dakunan kwana, wuraren cin abinci, filayen horaswa da kuma na’urorin samar da wutar lantarki.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here