Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta rushe wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnati, yayin da wasu daga ciki kuma za su curesu wuri daya domin rage yawan kudin da ta take kashewa na gudanar da su.
Ministan Yada Labarai na kasar Muhammad Sani Idris wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin a Abuja, ya ce sake tsara hukumomin ya biyo bayan umarnin da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya bayar na aiwatar da wani rahoton da aka gabatar shekaru 12 da suka gabata na gyare-gyaren ma’aikatu.
Karin labari: Masu gidajen burodi sun tsunduma yajin aiki a Najeriya
A shekarar 2012 ne tsohon Shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin da ake kira da “Orosanya” da ya gabatar da wannan rahoto don gudanar da gyare-gyaren ma’aikatu da zai baiwa gwamnati damar rage kashe kudi, sai dai tun bayan wannan lokaci gwamnatin Jonathan da ta kafa kwamitin da kuma ta Buhari da ta gaji rahoton ba su aiwatar rahoton ba.
Sai dai a cewar ministan na Yada Labarai, matakin ba zai kai ga rasa ayyukan ma’aikatan da ke aiki a hukumomin da gyaran zai shafa ba.
Karin labari: ‘Ƴan ƙwadago sun kutsa cikin majalisar dokokin Najeriya
Tuni dai fadar shugaban kasar ta fitar da sunayen hukumomin da matakin zai shafa, ciki har da NACA da NCDC da za’a curesu guri daya karkashin ma’aikatar lafiya, sannan an mayar da hukumar kula da ‘yan gudun hijira, karkashin hukumar bada agajin gaggawa NEMA.