Yajin aikin likitoci a Koriya ta kudu ya janyo mutuwar dattijuwa

Koriya ta Kudu, yajin aiki, mutuwar, dattijuwa, likitoci,
Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ƙaddamar da bincike kan mutuwar wata mata dattijuwa bayan da aka hana motar ɗaukan marasa lafiya shiga asibitoci da dama saboda...

Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ƙaddamar da bincike kan mutuwar wata mata dattijuwa bayan da aka hana motar ɗaukan marasa lafiya shiga asibitoci da dama saboda yajin aikin da likitoci suke a ƙasar, mara lafiyar ta mutu ne cikin motar bayan da zuciyarta ta buga.

Kusan kashi 70 cikin 100 na ƙananan likitoci na yajin aiki tun makon da ya gabata inda suke adawa da shirin horas da ƙarin likitoci.

Karin labari: Gwamnatin Najeriya za ta hade wasu hukumomi don rage kashe kudi

Matakin ya janyo matsi a ɗakunan bayar da agajin gaggawa inda gwamnati ke zargin likitocin da jefa rayuwar jama’a cikin haɗari.

Jami’an da ke da ƙwarewar ba da agajin gaggawa a birnin Daejon ranar Juma’a sun kira kusan asibitoci bakwai domin kai dattijuwar sai dai dukkan asibitocin sun ƙi amincewa a kai matar saboda rashin likitoci da kuma gadaje.

Daga bisani an kwantar da ita a asibitin jami’ar gwamnati, mintuna 67 bayan da ta fara kira domin neman agaji sai dai an bayyana cewa rai ya yi halinsa da isar su asibitin.

Karin labari: Gobara ta kone shaguna 50 a kasuwar ‘yan katako a jihar Kano

A ranar Talata ne jami’an gwamnati suka ce za su yi bincike a kan lamarin, rahoton kuma ya karaɗe kafafan yaɗa labaran Koriya ta Kudu.

Ana ganin wannan ne rashi na farko da aka alaƙanta da yajin aikin likitocin inda likitoci masu neman ƙwarewa da masu sanin makamar aiki ke zanga-zanga kan ƙudurin gwamnati na ƙara yawan likitoci saboda fargabar gogayya.

Yajin aikin dai ya sa an ɗage aikin tiyata sannan lamarin ya sa dole tura marasa lafiya zuwa wasu asibitoci, kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka rawaito.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here