Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta kone kantuna 21 a kasuwar ‘yan katako da ke Rijiyar Lemo a karamar hukumar Dala a Kano.
Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya shaidawa NAN cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 2 na safiyar ranar Litinin.
A cewar Abdullahi, “mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 2 na safe daga hukumar sadarwa ta Najeriya NCC cewa an samu tashin gobara a kasuwar ‘yan katako.
Karin labari: Tinubu ya gana da hamshaƙan ‘ƴan kasuwar Najeriya
“Mun yi gaggawar tattara jami’an mu zuwa wurin da lamarin ya faru, muka kashe gobarar domin kada ta bazu zuwa wasu shaguna,” inji shi.
Abdullahi ya ce shagunan 21 na kunshe ne a bangaren kayan daki na kasuwar.
Ya ce ba’a samu asarar rai ba, kuma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.