Masu gidajen burodi sun tsunduma yajin aiki a Najeriya

Burodi, kungiya, masu, gidan, yajin aiki, najeriya
Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya AMBCN, ta bayyana janye yajin aikin da ta shiga bayan wata tattaunawa da ta gudanar da jami'an ma'aikatar noma ta...

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya AMBCN ta ce ta dakatar da duk wasu ayyukanta daga yau 27 ga watan Fabarairu.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta ɗauki wannan matsaya ne bayan kammala wani taron gaggawa na musamman da ta kira domin matsawa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakin sauƙaƙa kasuwancin masu sarrafa fulawa a ƙasar.

Karin labari: Mutane 7 sun mutu a wajen sayen shinkafa a ofishin kwastan

Sanarwar ta ce duk wasu ayyukan haɗawa ko sayar da burodi ya kawo ƙarshe ne a jiya Litinin, 26 ga wata, kuma yajin aikin zai ci gaba har nan da mako ɗaya.

Wannan dai zai ƙara dagula lamura a ƙasar, daidai lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar – NLC ta kira zanga-zangar gama-gari.

Karin labari: “Mutane na iya mutuwa idan muka ci gaba da ɗagawa gwamnati ƙafa” – Joe Ajaero

Najeriya dai na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ya kai ga masu kamfanoni ƙara farashin kayan da suke samarwa sanadiyyar hauhuwar farashin kayan da suke amfani da su.

Fulawa na ɗaya daga cikin kayan masarufi da farashinsu ya yi tashin gwauron zabi tun bayan da ƙasar ta shiga cikin halin tangal-tangal na tattalin arziƙi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here