Mutane 7 sun mutu a yayin turmutsutsun da ya auku a lokacin da suke layin sayen shinkafar da hukumar kwastan ta kwato a jihar Legas.
A kalla Mutane 10 ne suka fito don sayen shinkafar da ofishin shiyya na kwastan da ke unguwar Yaba ta jihar Legas ta fitar don sayarwa, inda ta ke sayar da buhu mai nauyin kilo 25 na shinkafar a kan kudi naira dubu 10.
Karin labari: Fada ya barke tsakanin bangarorin ‘yan bindiga 2 a Jihar Zamfara
Hukumar kwastan din ta ce ta dauki matakin sayar da shinkafar da ta kwato daga maso fasakauri cikin farashi mai rahusa ne don saukakawa al’umma wahalar matsalar abinci da suka tsunduma ciki.
Da farko dai an fara aikin sayar da wannan shinkafar cikin kwanciyar hankali, a kan idon Kwanturola Janar na Kwastan Wale Adeniyi, amma sai daga bisani lamura suka rincabe, har ya kai ga turmutsutsu.
Karin labari: Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalan kotun koli 11
Rahotani sun ce wata mata mai juna biyu da wasu mutane 6 ne suka mutu a wannan al’amari na turmutsutsu, lokacin da wasu ‘yan tsagera dauke da makamai, cikin kakin soji suka so kutsawa cikin inda ake rabon da karfin tsiya.
Wadanda abin ya faru a kan idanunsu sun ce lamarin ya wuce yadda ake gani a hotunan bidiyon da suka karade shafukan sada zumunta na intanet.
Sai dai kakakin hukumar Kwastan, Abdullahi Maiwada ya ce ba zai iya cewa an samu asarar rai ba, abin da ya sani shi ne wasu mutane sun suma a lokacin turmutsutsun.