Fada ya barke tsakanin bangarorin ‘yan bindiga 2 a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga, sace, dalibai, makaranta
'Yan bindiga da suka sace wasu fadawan sarki a kauyen Gonin Gora na karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna ta arewacin Najeriya sun bukaci a biya su...

‘Yan ta’adda da dama ne suka mutu a wani kazamin fada da ya barke tsakaninsu a kauyen Hayin Alhaji da dajin Munhaye na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa gwabzawar ta faru ne a sakamakon yunkurin da wasu ‘yan bindiga daga jihar Katsina suka yi na yin garkuwa da wasu mazauna kauyukan Zamfara a karshen makon nan.

A cewar rahotannin bayan da ‘yan bindigar na Katsina su ka mamaye kauyukan na Zamfara ne, kasurgumin dan bindigar nan na jihar Ado Alero ya yi gaggawar kaiwa kauyukan dauki don dakile yunkurinsu na satar jama’a.

Karin labari: Ana zanga-zangar tsadar rayuwa a jihohin Edo da Osun

Shaidun gani da ido sun tabbatarwa manema labarai cewa a wannan yunkuri an gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin biyu wanda ya kai ga asarar rayuka, duk da cewa dai bangaren Ado Alero sun dakile shirin garkuwa da mutanen kauyen.

A halin yanzu, bayanai sun ce mazauna kauyukan da aka gwabza kazamin fadan sun shirya gudanar da binne gawarwakin ‘yan ta’addan da suka mutu, wadanda har zuwa yanzu ba’a kai ga tantance adadinsu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here