Ana zanga-zangar tsadar rayuwa a jihohin Edo da Osun

zanga-zanga, jihohi, Edo, Osun, Najeriya
Mambobin ƙungiyoyi masu zaman kansu sun bazu kan tituna a jihohin Edo da Osun a ranar Litinin suna zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya...

Mambobin ƙungiyoyi masu zaman kansu sun bazu kan tituna a jihohin Edo da Osun a ranar Litinin suna zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya kai kashi 29 cikin 100, tun bayan janye tallafin mai ne rayuwa ke ƙara tsada.

Masu boren sun bazu kan tituna a Benin da Osogbo, manyan biranen jihar Edo da Osun da ke kudancin ƙasar.

Karin labari: EFCC ta ƙwato naira biliyan 60 a cikin kwana 100 – Olukoyede

A birnin Benin, masu zanga-zangar sun yi tattaki daga dandalin Kings zuwa titin Akpakpava, suna ɗauke da kwalaye waɗanda aka yi wa rubuce-rubuce kan batun tsadar rayuwa da ‘ƴan ƙasar ke fuskanta da kuma buƙatar da ke akwai na magance matsalar yunwa a ƙasar.

A jihar ta Edo ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a zaben da ke tafe a jihar, Dakta Azemhe Azena na daga cikin waɗanda suka fito zanga-zangar, inda ya nemi gwamnati ta ɗauki matakan kawo ƙarshen tsadar rayuwa a ƙasar.

Karin labari: Ecowas ta ɗage wa Nijar da Mali da Burkina Faso takunkumai

A birnin Osogbo na jihar Osun, masu boren sun yi gangami a wurin shaƙatawa na Nelson Mandela, inda su ma suka yi kira ga gwamnati da ta kawo ƙarshen tsadar rayuwa.

A baya-bayan nan an yi irin wannan zanga-zangar a wasu sassan ƙasar, kamar a jihohin Legas da Neja da birnin Ibadan na jihar Oyo da kuma jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here