Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya NiMet, ta fitar da sanarwar hasashen samun mamakon Ruwan sama tare da gargadin mutane da fadakar da su kan su yi taka tsantsan bisa hasashen samun ruwa mai karfi daga yau Laraba 28 ga watan Mayu zuwa Juma’a 30 ga Mayu.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Talata, mamakon ruwan saman na iya haifar da ambaliya a sassan Najeriya.
SolaceBase ta ruwaito cewa, jihohin da ake kyautata zaton samun mamakon ruwan da ambaliya sun hada da: Bayelsa da Ribas da Delta sai Ondo da Edo da Akwa Ibom da Cross River da Imo da Abia, sai Birnin tarayya Abuja da Kaduna da Nasarawa da Kogi da kuma Neja.
NiMet ta kuma ce, Akwai yiwuwar a samu ruwan saman maras karfi a wasu sassan Najeriya, don haka ta ja kunnen mutane game da hadarin ambaliya, da iska mai karfin da lalacewar hanyoyin ababen hawa da kuma rage yawan gani ga direbobi yayin da ake yin ruwa wadanda ke iya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa da yin barazana ga rayuka da dukiyoyi.













































