Hukumar NAFDAC ta kama kwalin dunkulen Maggi na Naira Miliyan 4.5 a Jihar Sokoto

NAFDAC, Maggi Cubes
NAFDAC, Maggi Cubes

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC, ta kama kwali 24 na dunkulen Maggi  da ya kare, wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 4.5 a Jihar Sokoto.

Ko’odinetan hukumar ta NAFDAC a jihar, Mista Garba Adamu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai NAN a ranar Alhamis cewa, tawagar da ke sintiri na hukumar ta kama, yayin da aka kama mai shi tare da hukunta shi.

Karanta wannan: Kotu ta bawa Emefiele izinin fita daga Abuja

Adamu ya ce wasu ’yan kasuwa sun yi amfani da rashin tantance matakan da kuma kwanakin karewar kayayyakin da za’a yi amfani da su wajen kai kayayyakin da suka kare ko kuma sun kusa karewa zuwa kasuwanni.

“Wasu ‘yan kasuwa na da dabi’ar jibge kayayyakin da suka gama aiki ko sun kusa cikawa a kasuwannin Sakkwato da kewaye, wasu kuma ana kai su kasuwannin kan iyaka da karkara domin ci,” a cewar sa.

Ko’odinetan ya ja hankalin ‘yan kasuwa da su guji sayar da jabun abu ko marasa rajista, da kuma kayan da suka gama aiki ga al’umma, ya tabbatar da cewa hukumar NAFDAC za ta ci gaba da aiwatar da dokar a kowane lokaci.

Karanta wannan: Barkewar annobar Kwalara a Zambiya ta kashe Mutane sama da 400

Ya kuma bukaci ‘yan kasa da su rika duba matakan rajistar hukumar ta NAFDAC da kuma yadda ake kerawa da kuma kwanakin karewar kayayyakin kafin amfani da su.

Adamu ya yabawa hukumomin da ke aiki kafada da kafada da jami’an tsaro da kuma kungiyoyin ‘yan kasuwa da daidaikun mutane tare da kungiyoyi bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar NAFDAC wajen kare lafiyar al’umma kamar yadda NAN ta bayyana.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here