Barkewar annobar Kwalara a Zambiya ta kashe Mutane sama da 400

kwalara zambia
kwalara zambia

Kasar Zambiya na fama da barkewar cutar kwalara da ta kashe mutane sama da 400 kuma wasu fiye da 10,000 sun kamu da cutar, lamarin da ya sa hukumomi suka ba da umarnin rufe makarantu a fadin kasar bayan hutun karshen shekara.

Gwamnatin kasar Zambiya ta fara wani gagarumin aikin allurar riga-kafi, kuma ta ce ta na samar da ruwa mai tsabta har lita miliyan 2.4 a kowace rana ga al’ummomin da abin ya shafa a fadin kasar dakekudancin Afirka.

Karanta wannan: Barazanar ‘yan bindiga ta tilasta mutanen kauyukan Zamfara 10 tserewa

Yanzu haka hukumar kula da bala’o’i ta kasa ta bazu domin tallafawa.

Kwalara cuta ce mai sa gudawa wadda kwayoyin cutar ke yaduwa ta hanyar gurbataccen abinci ko ruwan sha. Ana alakanta cutar da talauci da kumarashin samun tsabtataccen ruwan sha.

Tun watan Oktoba cutar ta bulla a kasar Zambiya kuma mutane 412 ne suka rasa rayukansu, haka kuma mutane 10,413 suka kamu da cutar, kamar yadda hukumar kula da lafiyar jama’a ta Zambiya ta fitar a ranar Larabar da ta gabata, hukumar da ke kula da harkokin kiwon lafiya na gaggawa a kasar.

Karanta wannan: FEC ta amince da sama da Naira Biliyan 9.6 don inganta rayuwar ma’aikata

Ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce an samu bullar cutar kwalara a kusan rabin gundumomin kasar da kuma tara daga cikin larduna 10, kuma kasar da ke da kusan mutane miliyan 20 ana samun masu kamuwa da cutar sama da 400 a kowacce rana.

“Wannan annoba na ci gaba da yin barazana ga lafiyar al’ummar kasar,” in ji ministar lafiya Sylvia Masebo, inda ta bayyana ta a matsayin matsala dake addabar kasar baki daya.

Karanta wannan: Gobara ta Lalata kasuwar Panteka dake Kaduna

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce adadin mace-mace sanadiyar cutar ya kai kusan kashi 4 cikin 100 a cikin watanni uku “adadi mafi muni.” Idan aka kula da cutar, yawanci adadin mutuwar da ake samu baya wucekashi 1 cikin 100.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here