Mutumin da ya turo matarsa daga saman bene ya gurfana a kotu

Court Gavel
Court Gavel

Wani mutum mai shekara 42 ya gurfana a gaban wata kotu da ke Legas bisa zargin shi da lakaɗa wa matarsa duka, da kuma yi wa ɗansa targaɗe.

Dansanda mai gabatar da ƙara Raji Akeem ya shaida wa kotu cewa a ranar 8 ga watan Satumba mutumin mai suna Austin Anthony ya yi wa matarsa dukan tsiya sannan ya turo ta daga saman bene, inda ta faɗo ta karye a ƙafafunta biyu sannan ta samu raunuka.

Haka nan kuma a ƙoƙarin da ya yi na fizgo ɗansa ɗan wata 3, da ke goye a bayan matar tasa, ya ji wa jinjirin rauni ta hanyar gurɗe masa kafaɗa.

Mai gabatar da ƙarar ya ce Mr Anthony ya kuma yi barazanar kashe matar tasa da wuƙa.

Rigima ta tashi tsakanin ma’auratan biyu ne bayan da matar tasa ta zarge shi da gazawa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na miji kuma uba.

Waɗannan abubuwa dai sun saba wa sassa na 56, da 172, da 245 da kuma 246 na dokokin jihar Legas na shekara ta 2015.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta tuhumce-tuhumcen da aka yi masa.

Kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya ce kotun ta bayar da belin sa kan kuɗi naira 500,000 da kuma mutum biyu waɗanda za su tsaya masa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here