Yanzu-yanzu: Matatar Dangote ta sake kara farashin litar fetur zuwa Naira 1,175

Dangote Refinery sabo

Matatar Dangote ta sake kara farashin man fetur, wanda a turance ake kira Premium Motor Spirit (PMS), lamarin da ya zama karo na uku da aka kara farashin a cikin mako guda.

Matatar ta sanar da ’yan kasuwar man fetur wannan karin farashi a ranar Litinin, inda ta daga farashin fetur a matatar zuwa Naira 1,175 kan kowace lita, daga naira 995 kan kowace lita da aka sanar a ranar Juma’a.

Kamfanin ya bayyana cewa wannan karin farashi ya kai Naira 180, wanda yake kusan kashi 18.1 cikin dari a cikin kwanaki uku kacal.

Matatar ta kuma sake duba farashin man dizal, wanda a turance ake kira Automotive Gas Oil (AGO), inda ta mayar da farashin zuwa Naira 1,620 kan kowace lita.

A baya-bayan nan matatar ta kara farashin PMS (man fetur) zuwa Naira 995 kan kowace lita daga Naira 874 kan kowace lita a karshen mako, karin da ya sa farashin fetur a gidajen sayar da mai ya haura Naira 1,000 kan kowace lita a fadin Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here