Gwamnatin tarayya ta shirya gudanar da Kidayar Mutane a watan Aprilun 2023.
Shugaban hukumar Kidaya ta Kasa NPC Nasir Isah Kwarra, ne ya bayyana hakan a karshen wani taro da hukamar ta gudanar da shugabannin ta na Jihohi ta kafar Internet, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar a Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN ya rawaito cewa tun a shekarar 2006 ne aka gudanar da Kidayar mutane da gidaje, wadda tun daga wancan lokacin ba a kara yi ba.
Wata sabuwar kididdiga ta baya bayan nan da aka fitar a shekarar 2020 ta nuna cewa adadin al’ummar Najeriya a kiyasi ya kai Miliyan 206 da doriya.
A cewar Shugaban hukumar Kidayar za a gudanar da kidayar jama’ar ne bayan kammala Babban Zaben shekarar 2023.










































