Allah ya yi wa tsohon magatakardan Jami’ar Bayero ta Kano Alhaji Yakubu Ahmed Ibrahim, da aka fi sani da Y.A. Ibrahim rasuwa.
Wata majiyar daga ƴan uwan marigayin ta shaida wa Solacebase cewa ya rasu ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano AKTH yau Alhamis bayan ya sha fama da jinya.
Majiyar ta ce za a yi jana’izar marigayin ne a makabartar Farm Center, bayan an kammala yi masa sallar jana’iza da yammacin yau.
Marigayin dai, ya yi ritaya daga aiki a jami’ar Bayero a shekarar 1994.
Marigayi Y. A. Ibrahim, ɗan ƙabilar Ebira kuma ɗan asalin jihar Kogi, ya rasu ya bar ƴaƴa da jikoki da dama.













































