Sallar Tahajjud: hukumar Hisbah ta Kano ta tura jami’anta Masallatai don bada tsaro

HISBA Commander General 678x381 1
HISBA Commander General 678x381 1

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tura jami’anta masallatai da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar 44 domin tabbatar da bada tsaro don inganta zaman lafiya a lokacin Tahajjud da za fara a daren Alhamis.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban kwamandan hukumar, Dakta Harun Ibn-Sina ya fitar yau Alhamis.

Tahajjud, wadda kuma ake kira da Sallar dare, addu’a ce da musulmi ke yi a cikin kwanaki 10 na ƙarshen watan Ramadan domin neman yardar Allah.

Ibn-Sina ya ce kwanaki 10 na ƙarshen watan mai alfarma lokaci ne da musulmi ke shagaltuwa da Sallar tsakiyar daren.

Ya kuma gargadi ɓata gari da su guji tsoratar da masu ibada a lokacin Sallar ta Tahajjud ko aikata miyagun ayyuka, yana mai cewa duk wanda aka samu da irin wannan mummunar ɗabi’a zai fuskanci fushin mahukunt.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here