Ƴan kasuwar canjin kudi sun yi asara yayin da naira ke cigaba da murmurewa, N703 kan dala 1

naira, Dollar, ragu, kasuwa, canjin, kudade
A ranar Larabar da ta gabata ne darajar Naira ta ragu zuwa 1,500 a kasuwar hada-hadar canjin kudade.Farashin ya ragu da kashi 3.45 daga Naira 1,450 kan...

Izuwa yanzu Naira na cigaba da samun farin jini dakuma ci gaba da bunkasa a kasuwar hada-hadar kudi, inda ta kara daraja N703 kan kowacce dala a Kano ranar Juma’a.

Ana kwatanta ci gaban da aka samu wanda akwananin baya ake dillacin ta a N810 kan kowacce dala a ranar Laraba.

Masu gudanar da harkokin canji dake Wapa a karamar hukumar Fagge a Kano da suka zanta da Jaridar SOLACEBASE sun bayyana yadda ake siyan da dalar kan N698 da kuma farashin da ake sayar da su a kan N703 kan kowace dala, inda ya bar ribar nera N5.

Daya daga cikin ’yan kasuwar da ke Wapa, Adamu Danjuma ya shaida wa SOLACEBASE cewa da sanyin safiya ana siyar da dala kan Naira 718, amma jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a.

Da aka tambayi SOLACEBASE dalilin faduwar farashin dala, Danjuma ya ce abu ne mai sauki kan bukatar da akewa dalar.

‘’Ka ga a kasuwar, bukatar dala ta ragu matuka idan aka kwatanta da wasu kwanakin baya. Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, yawancin mu muna da dala amma ba kwastomomi kamar yadda muka samu tururuwar a mako guda da ya gabata,” inji Adamu Danjuma.

Hakazalika, wani dan kasuwa a titin Bompai daura da Central Hotel, Nura Baba, ya ce a halin yanzu yana sayen kudin gida a kan N700, kuma ya sayar da su kan Naira 707 kowace dala a ranar Juma’a.

Baba ya ce yawancinsu suna yin asara ne saboda sun sayi dala a kan kudi kusan Naira 800 amma yanzu ba su da wani zabi illa su sayar a kan farashi kadan.

Sai dai kuma an canza dala akan Naira 710 kan kowace dala, a kasuwar Mile One dake Legas ranar Juma’a.

A Unguwar Ikeja da ke Legas, Dillalan canjin suna canza dala a kan N700 kuma farashin sayar da su ya kai N710 kan kowace dala, inda ya bar ribar N10.

Idan dai za a iya tunawa, a makon da ya gabata, Naira ta yi rauni zuwa kusan N900 kan kowacce dala, sakamakon shirin sake fasalin kudin da babban bankin Najeriya ya yi, a inda hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki tayiwa dillalan canjin kudaden kasar waje takunkumi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here