Antony joshua ya jikkata a hatsarin mota a ogun, yayin da mutum biyu suka mutu

Anthony Joshua 2

Hadarin mota a Ogun ya rutsa da shahararren ɗan dambe a duniya, Antony joshua a ranar litinin a yankin Makun na jihar, a kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon hatsarin, yayin da Antony joshua ya samu raunuka.

Bayanan da suka fito sun nuna cewa motar da ke ɗauke da Antony joshua, wato Lexus Jeep mai lambar rajista KRD 850 HN, ta buge wata babbar mota da ke tsaye a gefen hanya.

Hatsarin ya faru ne kafin gidan mai na Danco da ke kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan a jihar Ogun.

Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya a jihar Ogun, Afolabi Odunsi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.

Ya bayyana cewa Antony joshua yana raye duk da raunukan da ya samu, yayin da mutane biyu suka mutu a hatsarin.

Hukumar kiyaye haɗurra ta tarayya ta ce za ta fitar da cikakken bayani kan yadda hatsarin ya faru a wani lokaci na gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here