Hukumar JAMB ta amincewa ‘yan kasa da shekaru 16 su rubuta jarrabawar UTME ta 2025

Jamb 1 2

Shugaban hukumar JAMB Farfesa Is-haq Oloyede ya ce, yara masu hazaka na musamman wadanda kasa da shekaru 16 za a ba su damar yin jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ke shirya wa.

Oloyede ya ce hukumar za ta zakulo dalibai masu hazaka tare da ba su damar yin jarrabawar shiga jami’a.

Karanta: Hukumar NUC ta dakatar da amincewa da wasu jami’o’i, ta kuma kara kudaden sarrafa su zuwa Naira miliyan 25

A cewar sa, irin wadannan dalibai dole ne su ci akalla kashi 80 cikin 100 a UTME da (WAEC), ko (GCE).

Oloyede ya sanar da hakan ne a wani taro tare da masu ruwa da tsaki da manyan masu ba da shawara na fasaha (CTAs) da dai sauransu .

A wata sanarwa da mai baiwa hukumar shawara kan harkokin sadarwa, Dr. Fabian Benjamin ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya ce shugaban hukumar ta JAMB ya dage cewa za a aiwatar da mafi karancin shekarun shiga manyan makarantu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here