Hukumar kula da jami’o’i ta kasa (NUC) ta dakatar da amincewa da bayar da lasisi ga jami’o’i masu zaman kansu na tsawon shekara guda duk da cewa ta kara kudin sarrafa jami’o’in daga naira miliyan biyar zuwa naira miliyan 25.
Dakatarwar shekara guda kan amincewa da sabbin jami’o’i masu zaman kansu da Hukumar ta yi ya fara aiki ne daga ranar Litinin 10 ga Fabrairu, 2025.
Najeriya na da jami’o’i masu zaman kansu guda 149 da gwamnatin tarayya ta amince da su ta hannun NUC tun daga 1999.
A cikin wata sanarwa mai taken “Dakatar da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya,” NUC ta kuma kara kudin sayen fom din neman kafa jami’o’i masu zaman kansu daga Naira miliyan 1 zuwa Naira miliyan 5.
Karin karatu: Hukumar NUC Ta Amunce da duk kwasakwasan jami’ar tarayya ta Gombe
Babban sakataren hukumar ta NUC, Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ya bayyana cewa hukumar na kokarin sake mayar da jami’o’i masu zaman kansu a Najeriya don inganta bukatun jama’a da kuma inganta hadin kan bangaren ilimin jami’o’i masu zaman kansu a cikin tsarin jami’o’in Najeriya (NUS).
Ya ce sake duba ka’idojin kafa jami’o’i masu zaman kansu, na da nufin tabbatar da cewa sabbin cibiyoyin da aka kafa za su iya magance kalubalen da ake fuskanta a karni na 21.
Hukumar ta kuma sanar da dakatar da ci gaba da gudanar da aikace-aikacen da ba a yi aiki ba, ciki har da na jami’o’i masu zaman kansu waɗanda ba su sami ci gaba ba ko gabatar da takardu ga hukumar sama da shekaru biyu.













































