INEC ta ɗebe kayan zabe masu muhimmacin daga ofishinta na Imo

INEC Mahmood
INEC Mahmood

Hukumar Zaben mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce ta kwashe kayan zabe masu muhimmanci daga ofishinta na jihar Imo sakamakon hari tare da lalata kayan da ke ciki, a yankin ƙaramar hukumar Isu.

Shugaban sashen wayar da kan masu zabe da yada labarai na hukumar ta INEC Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja.

“Saboda haka ne muka ɗauki matakan bai wa kayan zaben kariya, inda muka canza wa kayan zabe mazauni,” in ji shi.

Ya kara da cewa: “Haka zalika dukkan katin zaben da ba a karɓa ba, muna adanawa, sannan za a ƙaro jami’an tsaron don tabbbatar da an ci gaba da aikin rarraba katin ga masu shi, a harabar ofishin.”

Festus Okoye ya ce wannan shi ne karo na huɗu da aka kai hari ofishin INEC a jihar Imo da ke kudancin Najeriya, a ƙasa da makonni uku, bayan da aka kai makamancin wannan hari a ƙaramar hukumar Orlu da Oru dukkan su a jihar ta Imo.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here