Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya bayar da umarnin gudanar da bukukuwan babbar Sallah cikin yayanin da babu shagulgula sosai tare da dakatar da Hawan dawakai na hawan Bariki a dukkan masarautun jihar.
Umurnin ya biyo bayan iftila’in ambaliya da ya yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a garin Mokwa da kewaye na jihar.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abubakar Usman, a lokacin da yake sanar da wannan umarni a yau Laraba, ya ce an dauki matakin ne a matsayin girmamawa ga wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma ba da damar zaman makoki da addu’o’i da kuma jimami.
Da yake mika sanar da wannan mataki da gwamnatin ta dauka ga masarautu, sakataren gwamnatin jihar, ya kuma bayyana cewa, ambaliyar Mokwa na daya daga cikin mafi muni a jihar tsawon shekaru da dama da suka gabata, kuma ta yi sanadiyyar salwantar rayuka da gidaje da kuma ababen more rayuwa.













































