Mutane 11 sun mutu sakamakon ruftowar Yashi a Kaduna

Kaduna map (1)

Wasu almajirai 11 sun mutu yayin da wasu kuma mutum 7 suka jikkata bayan da kasa ta rufta masu a wani rami da suke dibar Kasa a kauyen ‘Yar Doka da ke karamar hukumar Kubau ta jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar ‘ƴan sandan jihar DSP Mansir Hassan, ne ya tabbatar da mutuwar su, inda ya ce almajiran sun rasu yayin da suke hakar kasar bulo a ramin.

Ya ce bayan samun bayanin jama’ar gari da jami’an tsaro suka garzaya domin kai daukin gaggawa wajen ceto wadanda ba su mutu ba, tare da tono gawarwakin wadanda suka mutu.

Hassan ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda ya kara da cewa, da misalin karfe 1:45 na rana, an samu bayanai daga Hakimin ‘Yar-doka, Alhaji Lawal Damau wanda ya sanar da rundunar kan faruwar iftila’in.

DSP Mansir Hassan ya yi bukaci iyaye da su rika sanya idanu kan wurare da ‘ya’yansu ke zuwa.

A cewarsa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin, inda ya ce hukumomin da abin ya shafa na bakin kokarinsu domin gano musabbabin faruwar lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here