Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar da ya kai kasar Faransa da Landan

Tinubu returns Tanzania Trip

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a Abuja bayan ziyarar aiki ta mako biyu da ya kai Faransa da Birtaniya.

Shugaban ya isa bangaren shugaban kasa na filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da ke Abuja a yammacin ranar Litinin da misalin karfe 9:50 na dare, kuma wasu daga cikin ministocinsa sun tarbe shi da suka hada da Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT), Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Femi Gbajabiamila, shugaban ma’aikatan sa (CoS), da dai sauransu.

tafiye-tafiyen da shugaban ya yi, wadanda ba a yi cikakken bayani a hukumance ba, sun haifar da cece-kuce game da yanayin da ake ciki a kasar nan.

Cikakken bayani na nan tafe…….

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here