Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi bai amince da kalaman da tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Janar Theophilus Danjuma ya yi a baya-bayan nan, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su kare kansu a halin da ake ciki na rashin tsaro.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, Gwamna Namadi ya yi gargadin cewa irin wannan kiran na iya haifar da hargitsi.
“Shi (Danjuma) babban jami’in tsaro ne, kuma ya kamata a mutunta shi, amma idan ya ce a bar ‘yan kasa su kare kansu, ina ganin zai haddasa rashin zaman lafiya. “Dole ne a yi nazarin kalamansa a hankali.”
Karanta: Hukumar kula da gidajen yari ta musanta fasa gidan yari a Kwara
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnati na aiki tukuru don inganta tsaron kasar nan, har ma ya bayar da misalin da kokarin da ake yi a Jihar Jigawa na yadda tsare-tsare da hada-hadar jama’a ke haifar da sakamako mai kyau.
“Lokacin da muka hau mulki mun yi amfani da dabaru da dama sannan muka kawo kwararru, mun kuma hada kan sarakunan gargajiya tare da kafa kwamitoci na dindindin domin tattaunawa da jama’a, yanzu sun fahimci fada ko kashe juna ba shine mafita ba,” inji shi. “Ba mu kai ga matakin cewa mutane ke bukatar kare kansu ba.”
Gwamna Namadi ya kuma bayyana goyon bayansa ga kafa rundunar ‘yan sandan jiha, yana mai cewa har yanzu ita ce hanyar da ta dace wajen magance kalubalen tsaron kasar.