Hukumar kula da gidajen yari ta musanta fasa gidan yari a Kwara

prison 600x430 (1)

Hukumar da ke kula da gidajen yari ta ƙasa (NCoS) a jihar Kwara ta bayyana cewa babu wani gidan yari da aka fasa, kamar yadda wani dandali a internet ya ruwaito.

Kakakin Rundunar, CSC Bamigbade, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce: “An jawo hankalin hukumar game da wani labari da aka buga a internet cewa fursunoni tara sun tsere yayin da aka fasa wani gidan yari a Kwara.

Bamigbade ya kara da cewa, “Wurin da aka ce an fasa gidan yarin, wuri ne na gwamnatin jihar Kwara, kuma take kula da shu, ya kuma sha bamban da gidan yari, domin nan ne cibiyar horar da yara ta Borstal da ke Ilorin, wacce ita ce wurin da ake tsare da yara kanana da ke karkashin ikon Hukumar Kula da Gyaran Najeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here