Tinubu zai dawo Najeriya yau – Fadar Shugaban kasa

Tinubu depart US 750x430

A yau ne ake sa ran shugaba Bola Tinubu zai dawo Najeriya bayan ya shafe kusan makonni biyu a kasar waje, kamar yadda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya tabbatar.

A wani takaitaccen sakon da aka fitar a ranar Litinin, Onanuga ya rubuta, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida a yau.”

Tun da farko dai, fadar shugaban kasar ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa shugaban ya ci gaba da gudanar da harkokin mulki duk da yana zaune a kasashen ketare.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis din da ta gabata, Onanuga ya ce, “Shugaban ya bar birnin Paris zuwa birnin Landan a karshen mako, ya kuma ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an gwamnati, inda yake sa ido kan muhimman al’amuran kasa, ciki har da umarni ga shugabannin tsaro don magance barazanar da ke kunno kai a wasu sassan kasar.”

Ya jaddada cewa rashin Tinubu na wucin gadi ne kuma “daidai da lokacin da aka sanar na kusan makonni biyu,” tare da dawowar sa a ranar 21 ga Afrilu, bayan hutun Easter.

Tinubu ya tafi birnin Paris ne a ranar 2 ga Afrilu, 2025, domin ziyarar da fadar shugaban kasa ta bayyana a matsayin ziyarar aiki ta mako biyu.

Karin karatu: Tinubu na ci gaba da tafiyar da harkokin mulki daga kasashen waje, yanzu haka ya bar Paris zuwa London – Fadar shugaban kasa

Tun bayan rashin Tinubu a kasar, ake ta samun yawaitar kashe-kashe da sace-sacen mutane da ‘yan bindiga ke yi a sassan kasar nan, musamman a jihohin Filato da Benue.

Shugabannin ‘yan adawa irin su Atiku Abubakar sun bayyana damuwarsu kan ci gaba da zaman shugaban kasar a kasashen waje, “yayin da Najeriya ke cikin yanayin zubar da jini”.

A ranar 16 ga Afrilu, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a shekarar 2023, ya nemi shugaban kasar da ya dakatar da komawarsa Faransa a cikin mawuyacin halin rashin tsaro a gida.

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce Tinubu ya ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an gwamnati tun bayan tafiyar sa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here