Tinubu ya yafe wa fursunoni 175 kamar yadda doka ta bashi dama

tinubu 2

Majalisar koli ta ƙasa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu na bayar da afuwar musamman ga fursunoni 175 a sassan ƙasar nan.

Wannan mataki na da nufin rage cunkoson gidajen gyaran hali tare da tallafa wa tsarin adalci mai gyaran hali domin sake farfado da rayuwar masu laifi.

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna yadda gwamnatin Tinubu ke haɗa adalci da jin ƙai, tare da ba wa waɗanda suka cancanta damar sake haɗuwa da al’umma bayan ɗaukar darasi daga kurakuransu.

Majalisar ta tattauna rahoton kwamitin da ke kula da bayar da afuwa na musamman, wanda babban lauya kuma ministan shari’a na ƙasa ya gabatar, inda aka bayar da shawarwari daban-daban kan rage hukunci da bayar da cikakkiyar afuwa.

Daga cikin mutanen da suka amfana, mutum 82 aka yi musu cikakkiyar afuwa, 65 aka rage musu hukunci, yayin da hukuncin kisa guda bakwai aka mayar da shi zaman gidan yari har abada.

Sai dai ba a bayyana sunayen waɗanda suka amfana da wannan afuwa ba.

Dokar ƙasa ta shekarar 1999 da aka yi wa gyara ta ba shugaban ƙasa ikon bayar da afuwa, sassauta hukunci ko mayar da hukunci ta hanyar tausayi.

Ana yawan aiwatar da wannan mataki ne bayan nazarin shawarwarin kwamitin da ke tantance halin mutum, shekarunsa, lafiyarsa, da halayensa yayin zaman gidan yari.

Majalisar koli ta ƙasa ta kuma amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan daga jihar Kogi a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, da Dakta Aminu Yusuf a matsayin shugaban hukumar ƙidayar jama’a ta ƙasa.

Haka kuma an tabbatar da nadin Alhaji Tonge Beta Bularafa a matsayin kwamishinan tarayya mai wakiltar jihar Yobe.

Haka nan, majalisar ta amince da buƙatar shugaban ƙasa ta bai wa mutane 959 lambobin yabo na ƙasa, ciki har da mutum 824 da suka cika ka’idojin cancanta da kuma 125 da aka ware na musamman, inda wasu daga cikin su, kamar marigayan Ogoni tara, za su samu lambar yabo ta mutunci bayan rasuwarsu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here