Da ɗumi-ɗumi: Majalisar Koli ta amince da naɗa sabon shugaban hukumar INEC

FEC FEC

Majalisar Koli ta Ƙasa ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan daga jihar Kogi a matsayin sabon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan bayanai da dabarun sadarwa, Mista Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ne ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan a gaban majalisar domin cike gurbin da Farfesa Mahmood Yakubu ya bari bayan kare wa’adinsa a watan Oktoban 2025.

Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya da rikon amana, yayin da dukkan mambobin majalisar suka goyi bayan nadin nasa cikin haɗin kai da lumana.

Shugaba Tinubu zai aika sunan Amupitan zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

An haifi Amupitan a ranar 25 ga Afrilu, 1967, a garin Ayetoro Gbede, ƙaramar hukumar Ijumu ta jihar Kogi, yana da shekara 58, kuma Farfesa ne na dokoki a jami’ar Jos da ke jihar Filato, inda ya karanci digiri da digirgir a fannin shari’a.

A halin yanzu, yana rike da mukamin mataimakin shugaban jami’ar Jos (a fannin harkokin gudanarwa), tare da zama shugaban majalisar gudanarwa ta jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke jihar Osun, kuma ya taɓa zama shugaban sashen dokar jama’a na jami’ar Jos.

Labari mai alaƙa: Da Ɗumi-Ɗumi: Farfesa Yakubu ya mika ragamar hukumar INEC ga shugabar riƙon ƙwarya

Bayan harkar koyarwa, Amupitan ya yi aiki a wasu kwamitoci da hukumomi, ciki har da cibiyar nazarin dokokin ƙasa, majalisar kula da horar da lauyoyi, da kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu.

Ya kuma wallafa littattafai da dama a fannin shari’a, ciki har da Ka’idodin Gudanar da Kamfanoni, Shaidar Takardu a Nijeriya, da Ka’idojin Dokar Kamfanoni a Nijeriya.

Farfesa Amupitan, wanda ya zama Lauyan Ƙasa (SAN) a shekarar 2014, ya fara aikin koyarwa tun daga shekarar 1989 bayan kammala hidimar ƙasa a hukumar wallafa ta jihar Bauchi.

Kuma yana da aure tare da yara huɗu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here