Jami’ar Ibadan (UI), Jami’ar Legas (UNILAG), da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ne aka bayyana a matsayin manyan jami’o’i uku da suka fi kowa a Najeriya a jerin sunayen Jami’o’in Duniya na shekarar 2026 da cibiyar ƙididdige jami’o’i ta Times Higher Education (THE) ta fitar.
Rahoton da aka fitar a ranar Alhamis ya nuna cewa Jami’ar Ibadan ta shiga tsakanin matsayi na 801 zuwa 1000 a duniya, inda ta sake zama jami’ar da ta fi kowa a Najeriya bayan shekaru biyu sai UNILAG da BUK suka biyo baya a matsayi na biyu da na uku bi da bi.
Binciken na bana ya haɗa jami’o’i 2,191 daga ƙasashe 115, inda aka yi nazari bisa fannoni guda biyar da suka haɗa da koyarwa, yanayin bincike, ingancin bincike, alaƙa da masana’antu, da kuma fahimtar ƙasa da ƙasa.
Jami’ar Ibadan ta tashi daga matsayi na huɗu a 2025 zuwa na ɗaya a wannan shekarar, inda ta kwace kambun daga Jami’ar Covenant da ta riƙe matsayi na farko a 2024 da 2025.
Rahoton ya nuna cewa UNILAG ta fi sauran jami’o’in Najeriya a fannin ingancin bincike, yayin da BUK ta fi kowa a fannin hulɗar ƙasashen duniya, sai kuma jami’ar Covenant kuma ta ci gaba da nuna ƙwarewa wajen hulɗa da masana’antu.
A fannin ƙasa da ƙasa, UI da UNILAG suna cikin rukuni na 801–1000, yayin da BUK da Covenant da Landmark suka kasance a tsakanin 1001–1200.
Wasu jami’o’i kamar Ahmadu Bello, Jami’ar Ilorin, Jami’ar Jos, Jami’ar Najeriya Nsukka, da Jami’ar Fasaha ta Minna suna cikin rukuni na 1201–1500.
Daga cikin jami’o’i 51 na Najeriya da aka saka a jerin, 14 sun faɗa cikin rukuni na 1501 sama, yayin da jami’o’i 27 ba su samu matsayi ba.
Jerin da Times Higher Education ke fitarwa na ɗaya daga cikin ginannun auna ingancin jami’o’i a duniya, kuma jami’ar da za ta shiga jerin dole ne ta koyar da ɗaliban digiri, ta wallafa aƙalla takardun bincike 1,000 daga 2020 zuwa 2024, tare da yin aiki a fannoni daban-daban na ilimi.













































