Shugaba Bola Tinubu ya umarci Rundunar Soji, ‘yan sanda da hukumomin leken asiri da su kaddamar da gagarumin aikin hadin gwiwa cikin gaggawa domin ceto mutanen da aka sace a baya-bayan nan a Jihar Niger.
Haka kuma, Tinubu ya umarci Shugabannin Tsaro da su rika ba shi bayanai akai-akai game da yadda aikin ceton ke gudana har sai an gano dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su.
Wannan bayanin yana kunshe a cikin wata sanarwa da Mai Baiwa Shugaban Kasa a bangare Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata a Abuja.
Tinubu ya nuna bacin ransa game da sace mutane da kuma kashe ‘yan kasa da babu ruwansu da miyagu suka yi a jihar, inda ya bayyana hararin a matsayin na rashin imani.
“Wadanda suka kai wannan hari kan ‘yan Najeriya da baza su iya kare kansu ba, makiyan zaman lafiya ne kuma makiyan bil’adama, wadanda ba za su tsira haka nan ba.
“Ina mika ta’aziyyata ta musamman ga iyalai da dangin wadanda aka kashe a wannan mummunan farmaki, kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba su hutu na har abada, sannan ya ba masoyansu juriyar dauke wannan rashi mai radadi,” in ji shi.
Shugaban ya tabbatar wa iyalan da abin ya shafa cewa Gwamnatin Tarayya zata ci gaba da jajircewa wajen ganin an dawo da ‘yan uwansu lafiya.
“Daukacin al’ummar kasar nan na tare da ku a wannan yanayi. Ba za mu huta ba har sai an dawo muku da ‘ya’yanku maza da mata, iyayenku mata da maza lafiya,” in ji Tinubu.
Ya umarci Dakarun Soji, ‘Yan Sandan Najeriya, Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro da na leken asiri da su hada kai wajen ganin an sako mutanen da aka sace.
Ya ce dole ne Shugabannin Ma’aikatan Tsaro su dinga sanar da shi halin da ake ciki akai-akai har sai an gano kowane mutum da aka sace.
“Ta’addanci ba zai tsorata Najeriya ba. Za mu kare al’ummarmu, mu kare yankunanmu, kuma mu mutunta martabar ran dan adam.
“Addu’o’ina suna tare da al’ummar Jihar Niger a wannan mawuyacin lokaci. Gwamnatin Tarayya ta tsaye tsayin daka tare da Gwamnatin Jihar kuma za ta ba da dukkan tallafin da ya dace domin taimakawa wajen farfadowa, agaji da kuma karfafa tsaro,” in ji shi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, a ranar Juma’a ne ‘yan ta’adda suka mamaye wasu masallatai da ke Gidan-Zana, kauyen Kpenya, gundumar Dekara, karamar hukumar Borgu da ke Jihar Niger, inda suka yi garkuwa da masallata da dama lokacin da ake sallar Juma’a. (NAN)













































