Gwamnatin Zamfara Ta Kwato Motoci 40 Daga Hannun Tsohon Gwamna Matawalle.

Jami’an tsaro a ranar Juma’a sun kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Mattawalle.

Rahotanni sun ce jami’an sun mamaye harabar gidan da ke mahaifar tsohon gwamnan na Maradun tare da kwashe motoci da dama.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan Zamfara kan kafafen Yada Labarai Suleiman Idris, ya ce an kwato kadarorin gwamnati da aka sace yayin samamen.

“Gwamnatin jihar Zamfara ta kawar da kai daga aikin rundunar ‘yan sandan Najeriya da ya kai ga kwato motocin da tsohon gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle ya wawure.”

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa “Da sanyin safiyar Juma’a ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kai farmaki gidan tsohon Gwamnan, inda aka kwato sama da motoci 40.

“’Yan sanda sun yi aiki da umarnin kotu kuma an samu takardar neman izini. Idan za a iya tunawa cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da tsohon Gwamna Bello Matawalle da mataimakinsa a hukumance da su dawo da dukkan motocin da suka batar cikin kwanaki biyar (5) na aiki.

“Saboda haka, ‘yan sanda sun nemi sammacin bincike wanda kotu ta ba su, wanda hakan ya sa suka kai farmaki gidan Matawalle dake karamar hukumar Maradun, da kuma wata maboyar da ba a tantance ba.

“Sama da motoci 40 ne aka kwato da suka hadar da motoci masu hana shigar harsashi guda uku da SUV guda takwas.

“Muna so mu yi kira ga al’ummar Zamfara da su kwantar da hankalinsu yayin da muke ci gaba da samun gagarumin ci gaba a fannin tsaro da kuma matsalar karancin ruwa a jihar.”

Da take maida martani kan lamarin, jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta yi Allah wadai da abin da ta bayyana a matsayin mamaya.

Kakakin jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce mamayar ta sabawa sashe na 34, 35, 37, 41, 42, da 43 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here