Labari da ke zuwa mana a yanzu haka ya kawo cewa shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan labarai na ofishin babban sakataren gwamnatin tarayya, Willie Bassey ya fitar a yau Juma’a, 9 ga watan Yuni, Channels TV ta rahoto.
Ya ce: “Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya, Mista Godwin Emefiele, CFR, daga ofis nan take.”













































