Mataimakin shugaban kasa, Kassim Shettima ya kaddamar da ofishin gwamnan Kano da aka yi wa kwaskwarima a gidan gwamnati da ke Kano.
Ginin ofishin ya hada da zauren majalisar zartarwa da dakin taro na majalisar zartarwa, da kuma sashin saukar manyan baki.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya tuna cewa tsohon shugaban mulkin soja na farko a jihar, marigayi Audu Bako ne ya gina shi a shekarar 1967.
Karanta wannan: Yanzu-yanzu: An rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo
Mataimakin shugaban kasar ya samu tarba daga Gwamna Abba Kabir da Kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas.
Sauran su ne Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril da Sanata Kawu Sumaila da kuma mataimakin gwamna Kwamared Aminu Abdussalam.
Karanta wannan: Cikin hotuna: Mataimakin shugaban kasa ya ziyarci Jihar Plateau
Shettima ya yaba da jajircewar da Yusuf ya nuna na ganin an kammala aikin a kan lokaci.
Ya bayyana cewa gyaran ofishin gwamnan da aka sanyawa na’urorin zamani zai samar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikata.













































